Jayyayan da ya faru a cikin Masanantn kwaikwayo da kuma rinjayar kafofin watsa labaru a shekar
Kafin shekara na 2015, ba na kula da wasannin Kannywood. Idan ina duban tashoshi akan tauraron ɗan Adam, bana tsaya ga kallon tashan Africa Magic na Hausa. Amma a shekaran da ya wuce, neman labaru akan kwaikwayon hausa ya zama wajibi domin aikin da na yi game da wani biki wanda ya shafi ʼƴan wasan kwaikwayon hausa (waton Kannywood). Ayyukansu ya bani shaʼawa sossai.
Idan ana magana akan harkar sinima ko Fim Village, babu inda ake samar da finafinai kaman Tinapa Studios na garin Calabar a Jihar Cross River. Wannan shi ya sa mutane da yawa sun yi murna a lokacin da aka samu labari cewa Gwamnatin Tarraya za ta gina Garin Kwaikwayo (waton Film Village) mai girman kadada ashirin, wanda aka yi niyyar zanawa kama waɗanda ke ƙasar China da India.
Wannan shawara ya samu matsala bayan an yi sanarwa cewa za a kafa wannan gini a garin Kano. Kano gari ne mai ingata alʼadun Hausawa da addinin musulunci. Gari ne mai raʼayin mazan jiya.
ADVERTISEMENT
Babban dalilin da ya sa an kawo shawara na kaddamar da wannan gini a garin Kano shi ne domin ƙarin tabbacin ingancin finafinai na Hausa da kuma ƙirkiran aiki. Amma wannan mafarki ya zama ba zai auku ba. Wannan ya faru bayan ɗan majalisar wakilaí Abdulmumin Jibrin ya sanar da jamaʼa akan aikin ginin garin fim a Kano. Mallaman addinni kamar Sheikh Abdallah Usman Gadan Kaya, sun tsayayya gwamanti.
Mun karɓi rahotanni da yawa cewa an soke shirin bayan shugaban ƙasa ya saurari koken jamaʼa musamman malaman addini da suka nuna adawa da lamarin. Malaman sun bayyana cewa gina ɗandalin zai gurbata tarbiyyar jamaʼa, kuma zai zama wurin alfasha da lalata. Idan muka haɗa fina-finan Nollywood da Kannywood, za mu lura da cewa Ƴan wasan Kannywood suna da tarbiyya da kuma hankali.
Mutane da dama sun yi mamaki da matakin da ƴan Kungiyar Masu hoto sun ɗauka a yayin da sun dakatar da Rahama Sadau domin wakan da ta yi da ClassiQ. Waɗanan matakai bai hana kafarfawa na fim masu shaʼawa a Kannywood. An saki wakoƙi, fim, rawa da sauran shiri masu kyau a Kannywood. Misalai su ne; Shiri kamar "Afra", "Ahmad", "Basaja Gidan Yari", "Iyalina", "Maula" da sauransu.
ncG1vNJzZmivp6x7scHLrJxnppdktaLB0ppmpJmeo8a4u86dZKOZqa6uuq3NZpuaZamWeqet0a5kmmWTnriquoymmKyZnpaur8DUp2Skr5GeuLit2KhknZldoMKurYyroKeika6us3nKmp2onpmjfHmCxqOecm8%3D